Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-16 15:34:16    
Shahararren babban dutse mai suna Lushan a kasar Sin

cri

Ganyen shayi da ake samu a kan dutsen nan na da kyau kwarai, sabo da wurin na da laima, kuma da akwai gajimare mai yawa da ke sauka a wurin. Irin wannan ganyen shayi na dutsen Lushan ba ma kawai ya sami karbuwa sosai daga masaya na kasar Sin ba, har ma ana sayar da shi zuwa kasashen Japan da Jamus da Korea ta Kudu da Amurka da Britaniya da sauransu. Farkon watan Afrilu na ko wace shekara lokaci ne mafi kyau da ake girbin ganyen shayin nan, yawancin masu yawon shakatawa su kan komar da ganyen shayin gida don ba da kyatarsu ga danginsu da aminansu.

Ban da wadannan kuma, tsire-tsire suna kamawa sosai a kan dutsen Lushan sabo da yanayi mai kyau da ake samu. Ga furanni masu kamshi kuma launuka iri daban daban wadanda suka game ko ina kan dutsen.

Lambun tsire-tsire na dutsen Lushan da aka kafa a shekarar 1934 lambun tsire-tsire ne da aka kafa a duk kasar Sin tun da dadewa. An kasa lambun a wurare daban daban kamar gandun daji da wuri mai dumi da wurin tsire-tsiren fadama da gonakin noman tsire-tsire da ake hada magungunan sha da makamantansu. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan ire-iren tsire-tsire na gida da waje da ke girma a wannan lambun ya wuce 3400, kai lalle suna da yawa.


1  2  3