Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-16 15:34:16    
Shahararren babban dutse mai suna Lushan a kasar Sin

cri

Dutse da ake kira Lushan cikin Sinanci wani shahararren dutse ne a karkarar birnin Jiujiang na lardin Jiangxi na kasar Sin da ke a tsakiyar Kogin Yangtse. A nan ne ake samun isasshen ruwan sama a duk shekara, yanayinsa kuma yana da kyau sosai. Musammam ma daga watan Maris zuwa watan Yuni, in an tsaya a gindin dutsen nan, za a ga gajimare da hazo na tashi daga dutsen zuwa samaniya, haka nan kuma in an tsaya a kan kololuwar dutsen, to, za a ga gajimare na tafiye a karkashin kafafuwa. A wani sa'i, gajimare ya game duk kololuwar dutsen, sa'an nan kuma ana yayyafi a gindin dutsen, kai lalle ne, wannan hali kayatarwa da ba a safai a kan iya ganin irinsa ba a sauran manyan duwatsu na duniya.

Malam Li Wenliang wanda ya girma a dutsen nan ya bayyana cewa, "idan wani ya sami damar zuwa dutsen Lushan don yin yawon shakatawa a tsakanin watan Maris zuwa watan Afrilu, abin da ya fi kyau shi ne ya kwana a kan dutsen. Bayan da ya tashi daga barci da asuba, ya fita daga kofar gidan, zai yi mamaki da ganin gajimare da hazo wadanda suka game duk dutsen nan, nan take mai yiwuwa ne, zai ji dadi ainun har ya manta inda yake."


1  2  3