Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-15 17:22:21    
Jami'ar Fudan ta yi kokarin daukar dalibai ta hanyar intabiyu

cri

Mr. Cai ya kara da cewa, ko da yake hanyar jarrabawa ta gargajiya ta ba yaran kasar Sin fasahar yin jarrabawa, amma yaran sun yi karancin kwarewar yin karatu da kansu da kuma yin amfani da fasahohin da suka koya a cikin zaman rayuwarsu, sa'an nan kuma, yaran sun fama da rashin hankali da lalacewar da'a, ba su saje da zamantakewar al'ummar kasa ba. Saboda haka, jami'ar Fudan tana fatan ja gorancin 'yan makarantar firamare da midil da su kawo wa ra'ayoyinsu sauye-sauye, su dora muhimmanci kan horar da kansu wajen kwarewar kirkire-kirkire da aikatawa ta hanyar intabiyu.

Wang Tianyu, wani dan makarantar sakandare, shi kuma ya shiga wannan intabiyu. Ko da yake bai ci nasara ba, amma yana ganin cewa, intabiyu din nan zai canje ra'ayinsa kan jarrabawar neman shiga jami'a, har ma hanyoyin karatu. Ya ce,

'ina tsammani tun daga makarantar sakandare ta aji na 1 da na 2 ne za a fara share fage ga intabiyu, a maimakon yin aikin shirya a cikin mako daya kafin intabiyu. Don cin nasarar intabiyu, a lokacin da a mai da hankali kan karatu, a sa'i daya kuma, za a sa hannu cikin harkokin zaman al'ummar kasa da jarrabawa iri daban daban cikin himma da kwazo. Sa hannu cikin irin wannan harkoki, ba ma kawai don neman samun lambar kyauta ba, har ma karfafa kwarewa.'

Sabuwar hanyar daukar dalibai da jami'ar Fudan ta bi ta sami amincewa daga mutanen rukunin aikin ba da ilmi da kafofin yada labaru da 'yan makaranta da iyayensu masu yawa, suna ganin cewa, za a karfafa hanyoyin daukar dalibai cikin jami'o'i da kwalejoji, a sa'i daya kuma, za a taka rawar ja goranci a fannin kara karfin ba da ilmi don karfafa inganci a makarantun firamare da na midil.(Tasallah)


1  2  3