Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-15 17:22:21    
Jami'ar Fudan ta yi kokarin daukar dalibai ta hanyar intabiyu

cri

Yanzu za mu soma karanta muku wani bayani da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya aiko mana, bayan da ya kai ziyara a shahararriyar jami'ar Fudan ta Shanghai. Kwanan baya, 'yan makarantar sakandare 300 sun shiga jami'ar Fudan ba tare da yin jarrabawar da aka yi a duk fadin kasar Sin ba.

Zhang Moran, wata 'yar makarantar sakandare na aji na 3, ta shiga intabiyu da jami'ar Fudan ta shirya a kwanan baya, a karshe dai, ta ci nasara. Game da wannan intabiyu, Zhang Moran tana tsammani cewa, irin wannan jarrabawa ta iya jarraba ingancin wani dan makaranta daga duk fannoni yadda ya kamata. Ta ce,

'a ganina idan wani ya sami maki mai kyau a cikin jarrabawa, ba tabbas ne ya gwada gwanintarsa a dukan fannoni ba. Shi ya sa irin wannan jarrabawa ta zama abin tilas, a lokacin da yake yin hira da saura, za a jarraba ko za su amince da shi ko a'a; in yana da dabara mai kyau, ko saura za su karbe ta ko a'a, duk wadannan suna da muhimmanci, za a iya gane su ta hanyar yin hira.'


1  2  3