Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-15 17:22:21    
Jami'ar Fudan ta yi kokarin daukar dalibai ta hanyar intabiyu

cri

A watanni 2 da suka wuce, jami'ar Fudan ta ba da labari na daukar dalibai ta hanyar intabiyu. Saboda ta yi suna sosai a kasar Sin, shi ya sa, da zarar ta ba da wannan labari, sai 'yan makaranta fiye da dubu 6 sun yi rajista. Kafin intabiyu, jami'ar Fudan ta shirya jarrabawa a rubuce tukuna, ta tabbatar da 'yan makaranta fiye da dubu 1 da su yi intabiyu, bisa sakamakin jarrabawa a rubuce.

A sa'i daya kuma, jami'ar ta kafa kungiyar masana masu kula da intabiyu da ke kunshe da shehun malamai fiye da 100. A ran da aka yi intabiyu, 'yan makaranta sun zabi masana 5 da su yi musu intabiyu ta hanyar jefa kuri'a, daga baya sun yi hira da kowane shehun malami cikin mintoci 15 daya bayan daya. A karshe dai, bisa yadda suka gwada gwanintarsu a cikin intabiyu, masanan sun zabi wasu 300 mafi nagarta, jami'ar ta daukar wadannan 'yan makaranta 300.

Mataimakin shugaban jami'ar Fudan Mr. Cai Dafeng ya bayyana cewa, a matsayin jami'in jami'a, ba ma kawai yana son san karfin 'yan makaranta a fannonin ilmi ba, har ma yana son san yaya suke, yaya suka girma, yaya ra'ayoyinsu suke da dai sauransu, shi ya sa, jami'arsu ta shirya wannan intabiyu da kanta, don jarraba 'yan makaranta daga dukan fannoni. Ya ce,

'mun biya wadannan manyan bukatu ne ta hanyar intabiyu. Da farko, muna fatan gano ra'ayoyin da 'yan makaranta suke tsayawa a kai, musamman ma ra'ayoyinsu kan zaman al'ummar kasa da kuma nauyin zaman al'ummar kasa. Na biyu, muna fatan sanin kwarewar 'yan makaranta a fannin nazari. Na karshe, mun dora muhimmanci kan fasahohin da suka samu daga wajen harkokin zaman al'ummar kasa.'


1  2  3