
Malam Wang Shoucong, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin dashe-dashe na ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ya bayyana cewa, don kara daga matsayin sanya ido ga bala'in abubuwa masu rai da shawo kansa, kasar Sin za ta yi kokarin kafa sabon tsarin kare tsire-tsire wanda gwamnatin ke aiwatarwa don bauta wa jama'a. Ya ce, "aikin kare tsire-tsire ba aikin yadada fasahar aikin noma ba ne, banban da haka aiki ne da gwamnatin za ta kula da shi. Dalilin da ya sa haka shi ne domin aikin nan ya shafi zaman lafiyar kasa da kwanciyar hankali na jama'a. Sabo da haka wajibi ne gwamnatin ta kula da aikin nan, kuma bai kamata a gudanar da shi ta hanyar kasuwanni ba."
Bayan haka Malam Wang Shoucong ya kara da cewa, bisa kasafin da ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin ta tsara, bayan kafuwar sabon tsarin kare tsire-tsire a kasar Sin, za a kafa tashoshin sanya ido kan miyagun kwari a sama da rabin gundumomi, za a bayar da yawancin labaru kan miyagun kwari kafin su haddasa bala'i ga aikin noma, za a kara kwarewa wajen magance manyan miyagun abubuwa masu rai da ake samu daga kasashen waje da dai sauran. (Halilu) 1 2 3
|