Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-12 16:59:38    
Kasar Sin za ta kafa sabon tsarin kare tsire-tsire

cri

Yanzu, kasar Sin ta gamu da bala'i mai tsanani da abubuwa masu rai suka haddasa a fannin aikin noma, kuma tana kara shan wahala daga wajen abubuwa masu rai da aka shigo da su daga kasashen waje. Irin wannan bala'i ba ma kawai ya kawo lahani ga cinikin amfanin gona ba, har ma a wani sa'i zai kai barzana ga zaman lafiyar jama'a. A cikin irin wannan hali ne, a kwanakin baya ma'aikatar aikon gona ta kasar Sin ta gabatar da sabon tsarin kare tsire-tsire da za a kafa nan da 'yan shekaru masu zuwa, don kara karewa wajen sanya ido ga bala'in abubuwa masu rai da kuma shawo kansu.

Tsarin kare tsire-tsire babban tsari ne da ake gudanar da shi wajen rigakafin bala'in kwari da shawo kansa ta yadda za a ba da tabbaci ga aikin noma. A cikin shekarun nan sama da 10 da suka wuce, kasar Sin ta riga ta kafa kwarya-kwaryar tsarin kare tsire-tsire da ke dacewa da raya aikin noma, kuma ta ci gajiyarsa sosai wajen girbin hatsi mai armashi da kara wa manoma kudin shiga mai yawa da samun ci gaba mai dorewa wajen bunkasa aikin noma.

Amma ya zuwa yanzu dai, kasar Sin tana daya daga cikin kasashen duniya da suka fi shan bala'i mafi tsanani irin na kwari da bera da ciyayi da makamantansu a fannin aikin noma. Yawan ire-irien abubuwa masu rai da ke jawo bala'i ga aikin noma ya kan wuce 1700 a ko wace shekara.


1  2  3