
Malam Zhang Runzhi, shehun malami da ke aiki a sashen nazarin ilmin dabbobi na cibiyar kimiyya ta kasar Sin ya bayyana cewa, "a sakamakon bunkasuwar cinikin waje da ake yi a tsakanin kasar Sin da kasashen waje, yawan miyagun abubuwa masu rai da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen waje ya karu da sauri. A cikin 'yan shekarun baya, an gano sabbin miyagun abubuwa masu rai da yawan ire-irensu ya kai 18 a kasar Sin. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an nuna cewa, wasu manyan abubuwa masu rai da aka samu daga kasashen waje su kan jawo hasarar kudin Sin Yuan biliyan 57 ga aikin noma a ko wace shekara."
An ruwaito cewa, kasar Sin tana baya-baya ainun wajen yin aikin kare tsire-tsire idan an kwatanta shi da na kasashe masu sukuni. Alal misali, yawan wuraren sanya ido kan kwari bai kai 5 a ko wadanne kadada miliyan 1 ba yanzu a kasar Sin, amma ya kai 60 a Japan, haka nan kuma ya kai 98 a kasar Korea ta Kudu.
1 2 3
|