Wani Rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan taswirar rarrabawar tafkokin Afrika ya bayyana cewa , har yanzu ba a hana raguwar ruwan tafkokin Afrika ba . Daga hotunan da aka dauka ta tauraron 'dan Adam ana iya ganin cewa , matsayin ruwan tafkoki masu yawa na Afrika ciki har da Tafkin Nakuru da Tafkin Chadi yana ragewa .
Wani kakakin Hukumar shirye-shiryen muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce , kusan dukannin tafkokin Afrika auna lalacewa . Wannan kakakin ya yi gargadi cewa , tafkoki albarkata masu daraja ne da mutanen Afrika suke dogara a wajen zaman rayuwa . Idan ba a iya kiyaye su sosai ba , to , ba za mu iya tabbatar da makasudin yalwatuwa na shekaru dubu na Majalisar Dinkin Duniya a shiyyoyin Afrika ba .
To, jama'a masu sauraro, shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Birkisu ce ta karanto muku . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .(Ado ) 1 2 3
|