A cikin 'yan shekarun da suka shige , tattalin arzikin kasashen Afrika ya kyautatu a kai a kai . A watan Afrilu na wannan shekara Kungiyar asusun duniya ta kiyasta cewa , a shekarar 2006 , yawan karuwar tattalin arzikin kasashen Afrika zai kai kashi 5.7 cikin 100 , wato ya fi na shekarar bara . A shekarar 2005 tattalin arzikin kasashen Afrika ya karu da kashi 5.2 cikin 100 . Amma duk da haka masu binciken al'amuran duniya suna ganin cewa , Karancin albarkatan ruwa mai tsanani mai yiwuwa ne zai kawo tasiri maras kyau ga yalwatuwar tattalin arzikin Afrika .
Yanzu matsayin ruwan tafkokin Afrika masu yawa suna ragewa . Tafkin Victotria dake iyakar tsakanin kasar Kenya da Uganda da Tamzania babban tafki mai ruwa maras gishiri na biyu ne a duniya . Amma tun daga shekarar 1920 matsayin ruwa na wannan tafkin ya rage da saurin gaske.
1 2 3
|