A cikin dogon lokacin da ya shige , Tafkin Victoria wata muhimmiyar hanyar ruwa ce a shiyyar Afrika ta gabas . Hanyoyin jiragen kasa suna hade da tashoshin ruwa masu yawa na Tafkin Victoria da birnin Dares Sallam da Mombasa da sauran biranen dake gabar teku . Idan za a jigilar kayayyakin kasuwa A Tafkin, to , da sauki ne ana iya sayar da su a tsakanin kasashe 3 wato Kenya da Tanzania da Uganda .
Saboda ruwan Tafkin Victoria ya ragu , shi ya sa yawan lantarki mai karfin ruwa na kasar Uganda ya ragu kwarai da gaske kuma ya kawo tasiri ga samar da lantarki ga kasar Kenya da Uganda . Sa'an nan kuma raguwar ruwa ya kawo tasiri mai tsanani ga aikin zirga-zirgar tafkin Victoria da aikin tashoshin ruwa . Bisa kididdigar da aka yi , an ce , yawan kayyayakin da aka jigilar a tafkin ya ragu da kashi 70 cikin 100 a shekarar 2005 . Jiragen ruwa masu daukar kayayyakin da wuya ne sun zame a tashoshin ruwa masu yawa .
Irin wannan Hali kuma ya auku a Tafkin Tankenika .
Galibin Cinikin kayayyakin da aka yi a tsakanin kasar Brundi da Congo (Kinshasa) da Tanzania da Zambia an yi shi ne ta hanyoyin ruwan Tafkin Tankenika . Amma aikin jigilar kayayyakin da ake yi a Tashar ruwan Bujunbura na kasar Brundi ya gamu da katanga saboda ragewar ruwan tafkin .
1 2 3
|