Lokacin da ya kai shekaru fiye da 40 da haihuwa, ya soma rubuta littattafan tarihi bayan aikinsa, ya yi editan littafin "Zhou Ji" wato "abubuwa dangane da daular Zhou" da "abubuwa dangane da daular Qin" bi da bi, sa'anan kuma ya gabatar da wadannan littattafai ga sarki, bayan da sarki ya karanta littattafan, sai ya nuna yabo sosai gare shi, kuma ya ba da umurni ga Si Maguang cewa, ya kamata ya ci gaba da aikinsa na yin editan bisa tsarin shekara shekara, har ma ya kafa wata hukumar kula da littattafai dominsa da kuma aika masa da wadanda ke iya ba shi taimako, a karshe dai Si Maguang ya kammala aikin rubuta kuma editan littafin "Zi Zhi tong Jian", an ce, takardun rubuce-rubuce na littafin nan na da yawan gaske , har ma sun cika dakuna guda biyu.
Ya kammala littafin "Zi Zhi Tong Jian"a shekarar 1084, yawan kalmomin da ya rubuta ya kai miliyan 3, wannan ne littafin tarihi na farko na kasar Sin, abubuwan da ya rubuta bisa tsarin shekara shekara sun shafi tarihin kasar Sin da ke da tsawon shekaru 1362.(Halima) 1 2 3
|