Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-10 16:50:27    
Wani mashahurin mutumin kasar Sin na zamanin da mai suna Si Maguang

cri
 

Amma , Si Maguang ya sami nasara ne musamman domin kokarin da ya yi fiye da na sauran mutane. A littattafan tarihi, an rubuta cewa, a lokacin da ya cika shekaru 7 da haihuwa, ya yi sha'awa sosai wajen karanta littattafan tarihi na zamani aru aru, domin kada ya bata lokaci, sai ya yi barci ta hanyar yin amfani da wani matashin da ya yi da guntun katako, ya rada masa suna cewa, matashin jawo hankali. Lokacin da ya yi barci da dare, da ya juya jikinsa, sai guntun katako ya mirgina , to ya tashi daga barci ke nan, nan da nan sai ya sauka daga gado ya soma karanta littattafai a karkashin hasken fitilu. Bisa kokarin nan ne, sai ya shiga jerin kushoshin kasa ta hanyar jarrabawar da aka yi masa a lokacin da ya cika shekaru 19 da haihuwa, sa'anan kuma ya zama wani mashahurin dan siyasa.

A cikin littattafan tarihi na gwamnati, Si Maguang shi gwarzon dan siyasa ne da ba ya ji tsoron kowa, kuma shi ne masanin tarihi da ke da wadatacen ilmi, ya ki cin hanci da rashawa, kuma ya yi kishin nazarin ilmi sosai. Ya yi zaman rayuwa cikin tsimi sosai. An yada cewa, lokacin da matarsa ta mutu, ba ya da kudin jana'izar, dansa Si Makang da danginsa sun yi fatan zai ari wasu kudadde daga wajen sauran mutane don yin jana'izar sosai, Si Maguang ya ki shawararsu, kuma ya horar da dansa cewa, ya kamata ya mai da hankali ga yin tsimi, a karshe dai ya jinginar da gonakinsa ya yi wa matarsa jana'iza cikin sauki, saboda haka , mutanen da suka zo daga bayansa sun ce, wannan abun misali ne da ya yi na jinginar da gonaki don yi wa matarsa jana'iza.


1  2  3