Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-10 16:50:27    
Wani mashahurin mutumin kasar Sin na zamanin da mai suna Si Maguang

cri

A gun tarihin ilmin kasar Sin, ba a iya manta da manyan littattafan tarihi guda biyu ba, wani littafi mai suna "Abubuwan tarihi domin tunawa", wanda Si Maqian ya rubuta kuma edita a karni na 2 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), wani daban kuma littafin da ake kira "Zi Zhi Tong Jian" wanda Si Maguang ya rubuta kuma edita a karni na 11. Yau bari mu bayyana wa masu karatu (ko masu sauraronmu ) wasu abubuwa dangane da Si Maguang da littafinsa mai suna "Zi Zhi Tong Jian".

An haifi Si Maguang a shekarar 1019 a wani gida mai arziki sosai na daular Son ta kasar Sin, tun lokacin da yake karami, ya sami tarbiyya mai kyau, kuma ya nuna hazikanci sosai. A tsakanin jama'ar kasar Sin, an yada wani labari dangane da shi a wurare masu yawa, wato labarin da ke da lakabi haka: Si Maguang ya rushe wata randar ruwa. A cikin labarin, an bayyana cewa, a lokacin da Si Maguang yake karami, ya yi wasa da wasu kananan aminansa a farfajiyar gida, a tsakiyar farfajiyar, an aza wata randar da ke cike da ruwa, wani karamin amininsa ya hau bakin randar ,amma ba zato ba tsammani ya fada cikin randar, sauran kananan aminansa sun ji fargaba, har ma ba su san yadda za su yi ba, amma Si Maguang dan karami sosai ya yi halin nutse, ya dauki wani babban dutse , ya rushe randa, har ruwa ya malala, ya ceci wanda ya fada cikin randar. Mai fasahar gargajiyar kasar Sin ya yi wani zane dangane da labarin nan, wato zane dangane da yadda dan yaro karami ya rushe randar ruwa don ceton amininsa. Sa'anan kuma an mayar da zanen nan don ya zama littafin karatu ga yara don soma wayar da kansu.


1  2  3