Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-09 15:51:21    
Lambunan shan iska na sarkunan kasar Sin a birnin Beijing

cri

Manyan wurare masu ni'ima na fadar nan su ne tudu mai suna Wanshou da tafki da ake kira Kunming a cikin Sinanci. Haka kuma ga wata doguwar baranda wanda tsawonta ya kai mita 728, wato ke nan ita baranda ce mafi tsawo a duniya. Har ma an taba shigar da ita cikin "Littafin Guinness na abubuwa masu bajinta ko al'ajabi a duniya".

Ban da wadannan kuma akwai wani shahararren gidan tiyata wanda shi ne tsohon gidan tiyata mafi girma a kasar Sin. Gidan tiyatar nan tana da bene uku, tsayinsa kuma ya kai mita 21. Fasalinsa na da ban mamaki, ba ma kawai an yi amfani da na'ura wajen daga labule da saukar da shi ba, har ma an iya jawo ruwa zuwa dakalin wasa. Bayan da madam Joanna Maskell, 'yar yawon shakatawa ta kasar Britaniya ta ziyarci wannan gidan tiyata, sai ta ce, "ko shakka babu, an yi sha'awar kallon wasannin fasaha da aka gabatar a gidan tiyatar nan, bayan da muka shiga cikin gidan, sai muka gano abubuwa masu ban sha'awa da yawa. Lalle ne, gidan nan ya shaku cikin zukatanmu sosai." (Halilu)


1  2  3