Ban da lambun shan iska na Beihai, akwai wata fadar hutun sarkin kasar a lokacin bazara wato "The Summer Palace" a Turance wadda ke yammacin karkarar birnin Beijing. An fara gina wannan tsohuwar fada ne a shekarar 1750. Malam Gao Dawei, mataimakin shugaban fadar nan ya bayyana cewa, bisa matsayinta na daya daga cikin tsoffin kayayyakin al'adu a duniya, an nuna yabo cewa, fadar hutun sarkin kasa a lokacin bazara ta birnin Beijing ta cancanci zama fada mafi kayatarwa da inganci da aka tsara fasalinta sosai a kasar Sin. Ya ce, "fadar hutun sarkin kasa a lokacin bazara fada ce mafi kyau da ke wakiltar lambunan shan iska na sarkunan kasar Sin a birnin Beijing, sa'an nan kuma fadar tana nan sumul garau har ba a iya samun irinta ba a duk lambunan shan iska na sarkunan kasar Sin a birnin Beijing.
Duk fadin fadar nan ya kai kimanin kadada 300. Ban da fadoji da rumfuna da husumiya da gadoji da aka gina a cikin fadar, kuma akwai dakunan ibada masu kayatarwa da wurare masu ban sha'awa na kauyuka.
1 2 3
|