Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-09 15:51:21    
Lambunan shan iska na sarkunan kasar Sin a birnin Beijing

cri

Yau sama da shekaru 800 ke nan da birnin Beijing ya zama hedkwatar kasar Sin, inda akwai tsoffin lambunan shan iska manya da kanana na sarakunan kasar Sin da yawansu ya zarce 10. Duk wadannan lambunan shan iska masu ni'ima ne da kayatarwa kwarai. Daga cikinsu, akwai wani lambun shan iska mai suna Beihai wanda shi ne ya fi dadewa a duniya. Madam Bai Zhenzhen, masaniyar ilmin tarihi ta cibiyar nazarin al'adu ta lambun shan iska na Beihai ta bayyana cewa, marigayi Hubilie, tsohon sarkin kasar Sin wanda ya kafa daular "Yuan" a karni na 13 ya zabi wannan fili da lambun shan iskar nan take, ya kafa hedkwatar kasarsa a kewayen lambun nan. Ta ce, "tun daga zamanin daular "Yuan", lambun nan ya yi ta zama lumbun shan iska ta sarakunan kasar Sin a zamanin daular "Yuan" da ta "Ming" da "Qing". Bisa tarihin duniya game da kafa hedkwatar kasa, ba safai a kan zabi wani lambun shan iska ya zama filin da sarkin kasa ya kebe a kewayensa don kafa hedkwatar kasarsa ba a duniya. "

A yanzu, duk fadin lambun shan iska mai suna Beihai ya kai kimanin kadada 70, haddin ruwa ya dauki sama da rabin fadin lambun nan. An gina fadoji masu kayatarwa da haikalai da ba hayaniya a cikin lambun nan yadda ya kamata. Akwai wani karamin tsibiri mai suna Qionghua a tsakiyar tafkin lambun, inda aka gina wata farar husumiya mai sigar hasumiyar Tibet. Sarkin daular Qing wanda ke bin addinin Buddah irin na Tibet ya aika da ma'aikata da suka gina ta. Wannan ya nuna cewa, sarkin kasar nan ya nuna girmamawa ga addinin Buddah, a bangare daya kuma an kara wa karamin tsibirin nan abu mai ban mamaki.


1  2  3