
Daga shekara ta l954, Mr.Samaranch ya fara hau dakalin siyasa ta hanyar wasan motsa jiki. A shekara ta l966, an zabe shi da ya zama mamba na kwamitin wasan Olimpic na duniya, daga nan ne a cikin shekaru 35 da suka shige, ya fara yin aiki a cikin kwamitin wasan Olimpic na duniya.
Kuma a shekara ta l980, Mr.Samaranch ya zama shugaban kwamitin wasan Olimpic na duniya.
Daga shekara ta 2001,wannan tsohon shugaban kwamitin wasan Olimpic na duniya ya yi ritaya daga mukamin shugaban kwamitin nan, amma koda yake ya yi ritaya daga mukaminsa,amma shi ya ci gaba da nuna sha'awarsa ga aikin wasan motsa jiki. Bugu da kari kuma yakan kai ziyara a kasashe daban daban don ci gaba da ba da taimakonsa kan sha'anin wasan motsa jiki na duk duniya.(Dije) 1 2 3
|