Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-09 15:45:08    
Tsohon shugaban kwamitin wasan Olimpic na duniya

cri
Jama'a masu karatu, yanzu za mu gabatar muku da wani bayanin da wakilin kasar Sin ya rubuta game da halin tsohon shugaban kwamitin wasan Olimpic na duniya. A ran 24 ga watan jiya, a babban hotel na Beijing, tsohon shugaban kwamitin wasan Olimpic na duniya Mr.Samaranch ya gana da maneman labaru na kasar Sin. Inda ya gaya wa maneman labarunmu cewa, Ina fatan a shekara 2008, a lokacin da birnin Beijing yake shirya wasan Olimpic na duniya na karo na 29 zan zo birnin Beijing don kallon wasa.Kuma ina fatan bayan za a kammala wannan wasa, sai dukkan mutane su iya cewa, kai wannan wasan Olimpic da birnin Beijing ya shirya ya fi na kowanen wasan Olimpic da aka shirya.

A shekara ta l996, 'yar wasan kwallon tebur ta kasar Sin mai suna Deng Yaping ta sami lambawan a cikin wasan Olimpic na duniya da kasar Australia ta shirya, sai wannan tsohon shugaban kwamitin wasan Olimpic shi kansa ya mika wa Deng Yaping lambar yabo. Daga nan ne mutane na kasar Sin sun san wannan tsoho mai kirki haka.


1  2  3