Mr Hu Jintao ya kuma bayyana cewa, a cikin shekaru 27 da suka wuce tun bayan da kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka har zuwa yanzu, kodayake huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta sha wahaloli da yawa , amma ta kara samun bunkasuwa daga dukan fannoni. Sada zumunci a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka buri daya ne da jama'ar kasashen biyu suke yi, yin hadin guiwar samun moriyar juna zabi ne mai gaskiya da kasashen biyu suka yi. Game da wannan, Mr Hu Jintao ya gabatar da ka'idoji guda 6, ya bayyana cewa, na farko, a kara fahimtar juna da kuma kara fannonin samun ra'ayi daya da kuma kafa huldar hadin guiwa mai amfani a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka cikin dogon lokaci. Na biyu, a yi amfani da sararin da aka samar da kuma bude tunani da inganta da habaka tushen yin hadin guiwar tattalin arziki da ciniki, Na uku, a bi ka'idoji sosai da kuma aiwatar da alkawari da kuma daidaita batun Taiwan bisa yarjejeniyoyi guda uku da aka daddale a tsakanin kasashen biyu. Na hudu, yin shawarwari sosai da kuma fuskatar kalubale da kara inganta ma'amala da daidaituwa a kan manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya shiyya. Na biyar, yin koyi da juna da samar da juna karin taimako da kuma kara inganta ma'amalar zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu. Na shida, yi wa juan girmamawa da yin zaman daidai wa daida, lura da kuma daidaita bambancin da ke tsakaninsu yadda ya kamata .
A dinar daren kuma, Mr Hu Jintao ya bayyana babbar manufar kasar Sin ta neman samun bunkasuwa a nan gaba.(Halima) 1 2 3
|