Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-21 17:05:45    
Mr Hu Jintao ya gabatar da ka'idoji 6 na raya huldar hadin guiwa mai amfani da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka

cri

A cikin jawabin fatan alheri da Mr Kissinger ya yi, ya bayyana cewa, idan ba a yi hadin guiwa sosai a tsakanin kasar Amurka da kasar Sin ba, to da wuya za a iya cim ma burin kafa wani cikakken tsari mai kyau ga kasa da kasa. Mr Kissinger ya nuna yabo ga kasar Sin saboda ta bi hanyar raya kasa cikin lumana, har ma ya nuna yabo sosai ga ziyarar da Mr Hu Jintao yake yi a wannan gami a kasar Amurka. Ya bayyana cewa, ya shugaba , ziyarar da kake yi a wannan gami ta sa zumuncin da ke tsakanin kasar Amurka da kasar Sin za ta kara ingantuwa, kasashen biyu za su yi kokari tare don ba da gudumuwa ga samun zaman lafiya da ci gaba a duk duniya.

Mr Hu Jintao ya bayar da jawabinsa da ke da lakabi haka: sa kaimi ga yin hadin guiwa mai amfani a tsakanin kasar Sin da Amurka daga dukan fannoni, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, a cikin gida, za ta mai da hankali sosai ga ayyukan raya kasa, kuma da zuciya daya ce ta nemi samun bunkasuwa, a wajen kasashen duniya kuma, za ta yi iyakacin kokari don kiyaye zaman lafiyar duk duniya da sa kaimi ga samun bunkasuwa gaba daya. Ya bayyana cewa, dawainiyar yanzu da kasar Sin take fuskantar  cikin gaggawa ita ce, za ta mai da hankali sosai ga raya tattalin arziki da kuma kara kyautata zaman rayuwar jama'a. Kasar Sin ta fi bukatar muhallin zaman lafiya na duniya. Mun gabatar da cewa, muna raya kasa ta hanyar kiyaye zaman lafiyar duniya, sa'anan kuma za mu sa kaimi ga samun zaman lafiyar duniya ta hanyar samun bunkasuwarmu.


1  2  3