Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-21 10:55:07    
Kungiyar wasan iyo ta kasar Sin ta kara aniya a cikin gasar cin kofin duniya ta wasan iyo na gajeren zango

cri

Ban da wannan kuma, sabon babban malamin koyarwa mai suna Zhang Yadong na kungiyar wasan iyo ta kasar Sin shi ma ya gamsu kwarai da gaske da ganin kyakkyawan sakamako da ' yan wasan suka samu. Ya fada wa wakilinmu, cewa :'Idan an duba gasannin wasannin motsa jiki na Olympics da aka yi a da, ana iya ganin, cewa ' yan wasa da yawa na kasar Sin sukan ji tsoro da kasa samun aniya. Amma a wannan gami fa, ' yan wasa maza da mata dukkansu sun fid da tsoro kuma tare da nuna kwarewa a gun gasar.'

Nasarorin da ' yan wasa na kasar Sin suka samu, ba ma kawai suka kara aniyarsu wajen samun lambobin yabo a gun wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a nan Beijing ba, har ma suka shere jami'an da'irar wasan iyo ta duniya. Mustapha Larfaoui, shugaban hadaddiyar kungiyar wasan iya ta duniya ya hakkake, cewa ' yan wasa na kasar Sin za su iya samun haskakkun nasarori a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a shekarar 2008 a Beijing. ( Sani Wang)


1  2  3