An kawo karshen gasar cin kofin duniya ta 8 ta wasan iyo na gajeren zango da aka yi kwanakin baya ba da dadewa ba a birnin Shanghai na kasar Sin. Kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya da dama. Lallai wannan ya sa kaimi ga ' yan wasan iyo na kasar, wadanda suka lashi takobi don samun manyan nasarori a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a shekarar 2008 a nan Beijing.
Sanin kowa ne, har kullum a kan ba da lambobin zinariya da yawa ga ' yan wasan iyo, wadanda suka zama zakara a gun kananan wasanni iri daban daban na iyon. Amma kuwa, nasarorin da ' yan wasan iyo na kasar Sin suka samu ba su kai a zo a gani ba. Alal misali : a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics da aka yi a shekarar 2004 a Aden na kasar Girka, ' yan wasan iyo na kasar Sin sun samu lambar zinariya guda daya da kuma wata lambar azurfa kawai ; kuma a gasar cin kofin duniya ta wasan iyo da aka yi a shekarar 2005, ba wanda ya samu lambar zinariya. Amma, a gun gasar cin kofin duniya ta 8 ta wasan iyo na gajeren zango da aka kammala kwanakin baya ba da jimawa ba, ' yan wasa na kasar Sin sun samu lambobin zinariya guda biyar, da lambar azurfa guda daya, da kuma lambobin tagulla guda 6 dungum. Ko shakka babu wannan ya sa babban kaimi gare su wajen samun manyan nasarori a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a shekarar 2008 a nan Beijing.
1 2 3
|