A gun gasa cikin zazzafan hali da aka yi a wannan gami, tsohuwar ' yar wasa mai suna Qi Hui ta samu lambobin zinariya guda uku a wasan gauraye na mata na tsawon mita 200 da 400 da kuma wasan kwado, lallai ta zama wata tauraruwa a gun gasar din. Da take hangen nesa ga taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a shekarar 2008 a nan Beijing, wannan shararriyar ' yar wasa ta fadi, cewa: ' A matsayin wata tsohuwar 'yar wasa, na ji raunuka da yawa a jikina. Amma duk da haka, zan iya mai da hankali kan jikina a cikin shekaru biyu masu zuwa don gudun jikata lokacin da nake yin horo ko gasa. Na lashi takobi wajen samun sakamako mafi kyau a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing'.
Daga nasu wajen, lallai ba a tafi an bar ' yan wasa samari baya ba. Kungiyar kasar Sin ta tura ' yan wasa 43 don halartar wannan gasa, wadanda kuma sama da rabinsu samari ne. Malamin koyarwa mai suna Tao Rong na kungiyar kasar Sin ya fadi, cewa :'Wassu ' yan wasa samari, wadanda dan wasa mai suna Wang Qun ke wakiltarsu sun samu babban ci gaba a shekara daya da ta shige. Wannan dai ya alamanta, cewa ya kasance da dimbin magadan nagartattun ' yan wasan iya a kasar Sin. Bisa wannan hali dai, mukan tsara musu shirin horo bisa matsayin da ya dace da su, ta yadda za su samu nasarori masu gamsarwa a gun taron wasannin Olympics na Beijing'.
1 2 3
|