A lokacin da shekarunsa na haihuwa suka wuce 30, ya tsai da wani kuduri cewa, zai shiga jami'ar koyar da ilmin wasannin sinima ta hanyar jarrabawa , a karshe dai ya shiga jami'ar koyon ilmin nuna wasannin sinima, a cikin shekaru goma da suka wuce, dan wasa Tang Guoqian bai nuna wasannin sinima ba, 'yan kallon kasar Sin sun kusan mantawa da shi.
A shekarar 1990, Tang Guoqiang ya sami damar nuna wasannin sinima, wato ya shiga aikin daukar wata sinimar TV, ya zama wani mashahurin mutumin kasar Sin na zamanin da, wato Zhu Geliang, ya yi kokarin aiki, ya soma kwarewa, kai, ya sami nasara, a kai a kai ne 'yan kallon kasar Sin suka amince da shi wajen nuna wasannin sinima.
Ba sau daya ba ba sau biyu ba Mr Tang Guoqiang ya fiyo a matsayin tsohon shugaban kasar Sin Mao Zedong a cikin sinima, lokacin da ya bayyana abubuwan da ya ji a cikin sinimar da ya yi, ya bayyana cewa,na sami fa'ida da yawa daga wajen manyan shugabanni, shi ya sa ina son in nuna wasannin da suka shafe su a fannoni da yawa, dukan wadannan sun kara daga matsayina wajen nuna wasannin sinima
Mr Tang Guoqiang ya bayyana cewa, tabbas ne wani mutumin da ke da tsayayyar niyya zai cim burinsa a karshe.(Halima) 1 2 3
|