Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-20 17:37:50    
Wani mashahurin dan wasan sinima na kasar Sin mai suna Tang Guoqiang

cri

Kafin shekaru 30 da suka wuce, Mr Tang Guoqiang ya soma aikin nuna wasannin sinima , kuma ya zama dan wasan sinima da ke samun kauna sosai daga wajen 'yan kallo a kasar Sin.

Mr Tang Guoqiang yana da shekaru 53 da haihuwa, idannunsa na da kaifi sosai, daga cikin wadanda ke da shekarun haihuwa daya da shi, ya fi nuna halin kuzari sosai da sosai . Kafin shekaru 30 da suka wuce, karo na farko ne Mr Tang Guoqiang ya nuna wasan sinimar da ke da lakabi haka, "Guguwar da aka yi a kudancin teku na kasar Sin", ya zama wani sojan ruwa a cikin sinimar. A shekarar 1979, Tang Guoqiang ya shiga aikin daukar wasan sinimar da ke da lakabi haka: Wani karamin fure. Sinimar ta yi masa tasiri mai muhimmanci a duk rayuwarsa. Sinimar ta bayyana yake-yaken da aka yi, amma ita ma ta bayyana soyayyar da ke tsakanin mutane. A cikin sinimar, Mr Tang Guoqiang ya zama wani soja mai suna Zhao Yongsheng da ke cike da kuzari sosai, a cikin sinimar, ba sau daya ba ba sau biyu ba kuma musamman ne aka nuna fuskarsa mai kyaun gani da ke haskaka mutane. Sinimar nan ta mai da Mr Tang Guoqiang don ya zama wakilin samarin da ke cike da kuruciya sosai a wancan zamani a kasar Sin, kuma ya zama mutumin da 'yan kallon sinima suke matsanancin kishi. Sa'anan kuma, a cikin sinimar da ke bayyana wata tatsuniya mai lakabi haka: Gimbiyar dawisu, ya zama wani dan sarki na kabilar Dai, lokacin da ya waiwayi abubuwan da ya taba yi a farkon lokacinsa na nuna wasannin sinima, ya bayyana cewa, a wancan zamani, na yi komai wajen nuna wasanni, na yi na yi kamar duk yadda aka gaya mini kawai.


1  2  3