Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-20 17:37:50    
Wani mashahurin dan wasan sinima na kasar Sin mai suna Tang Guoqiang

cri

Ya yi tsammanin cewa, zai sami komai lami lafiya a duk rayuwarsa ta nuna wasannin sinima, amma ba zato ba tsammani 'yan kallon sinima na kasar Sin sun kyale shi da sauri, kuma lokacin can ya yi daidai da lokacin da aka nuna sinimar kasar Japan da aka yi masa lakabi "Samame", a cikin sinimar, wani dan wasa na kasar Japan ya nuna wasanni dangane da wani dan sanda , ya sa 'yan kallon kasar Sin suka kaunarsa sosai da sosai, amma da suka waiwayi Tang Guoqiang , sai suka gano cewa, wai ba dan gaye ne sosai gare su ba wajen nuna wasanni a cikin sinima, sun ce, yana da fuska mai kyaun gani, amma bai iya nuna wasanni sosai ba, ra'ayin nan ya ba da tasiri sosai ga wadanda ke ba da jagoranci wajen nuna wasannin sinima, shi ya sa Mr Tang Guoqiang ya rasa damar nuna wasanin sinima da yawa.

A shekaru 80 na karnin da ya shige, Mr Tang Guoqiang ya yi fatan zai zama wani soja a cikin wata sinimar TV , amma an ki shi, shi ya sa ya rasa wannan damar . Game da hasarar da ya ci, ya bayyana cewa, wannan ne kashi mai muhimmanci ga duk zaman rayuwarsa, kuma ya samar da abubuwa masu yawa dangane da zaman rayuwa gare shi wajen nuna wasannin sinima. Ya bayyana cewa, in wani dan wasa bai taba bin hanya mai kalwade-kalwade ba , kuma bai taba shan wahaloli da yawa ba, to a cikin idannunsa, har abada ba su iya bayyana halin da ake ciki na cin daci da tsami ba, duk fasahohin da ya samu ya same su ne daga duk abubuwan da ya yi da saurarar su da ganinsu da koyonsu da kuma rubuta su da dai sauransu.


1  2  3