Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-17 17:53:07    
Zantutukan da aka yi kan nasara da hasara da aka samu bisa sakamakon samun makaurata na kasashen Afrika

cri

Kungiyar hakkin Dan Adam na kasa da kasa ita ma ta soma kira ga  gwamnatocin kasashen yamma da su dakatar da kwace albarkatan kwadago da kwararru na kasashen Afrika.

Wuraren da makauratan kasashen Afrika suka sauka ba kasashe masu wadata na yamma kawai ba. Dayake kasashe masu tasowa suna butakar makauratan da ke da kwarewar aiki, shi ya sa makaurata da yawa suna son kaurarsu zuwa wasu kasashen Afrika da ke da dan wadata, kamar su kasar Arfika ta kudu da Nanibiya da Botswana da sauransu. Babban dalilin da ya sa makaurata na kasashe masu fama da talauci suke kaura zuwa kasashen waje , shi ne saboda rashin aikin yi da albashi kadan.

An kira samun nasarori gaba daya a kan batun makaurata. A gun taron kasa da kasa da aka kira a birnin Brushel a watan jiya dangane da makaurata da samun bunkauwa , an kara da cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara hadin guiwarsu ta yadda za a daidaita kasuwannin kwadago na kasashen duniya don daidaita matsalolin da aka samu saboda makaurata da kuma cim ma burin samun nasarori gaba daya.(Halima)


1  2  3