
Kasashe masu ci gaba su ma suna kasancewa da halinsu na fannoni biyu, a wani fanni, suna fatan kasashe masu wadata za su dauki manufofin nuna sassauci kan makaurata, ta haka, za su iya kara samun kudadden musaya, a sa'I daya kuma za su iya koyo da kuma shigar da fasahohin kimiyya na zamani daga kasashe masu wadata, A wani fanni daban, a wajen sassan da suka yi karancin kwararru, kasashe masu tasowa su ma sun kai suka ga kasashe masu ci gaba saboda sun kwace kwararrunsu, wannan ya kara tsananta rikicin da suke gamuwa da shi.
A watan jiya, Makauratan kasar Kenya sun kafa wata kungiya, wadda ta tsai da kuduri cewa, za ta zuba jari da yawansu zai kai kudin Amurka dolla miliyan dari ga kasar Kenya a cikin shekaru biyar masu zuwa don raya tattalin arzikin kasar. Kafofin watsa labaru na kasar sun nuna yabo sosai ga wannan.
Kasashen Afrika sun yi farin ciki tare da damuwa. Manazartan al'amura na yau da kullum sun bayyana cewa, makauratan da ke zama a kasashen waje sun kawo moriyoyi da yawa ga kasashen Afrika, amma batun makaurata shi ma ya kawo babban kalubale ga wadannan kasashe wajen kiwon lafiya da sauran fannoni, saboda haka ya kamata kasashen Afrika su nemi hanyar da za su bi don daidaita batun.
1 2 3
|