Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-17 17:53:07    
Zantutukan da aka yi kan nasara da hasara da aka samu bisa sakamakon samun makaurata na kasashen Afrika

cri

A kowace shekara, domin neman samun sabon zaman rayuwa ne, samari da yawansu ya kai dubu gomai na kasashen Afrika ke gujewa  hadarin fadawa cikin manyan igogin ruwa na tekun Bahar Rum,domin  ketarewa zuwa kasashen Turai , wato sun shiga cikin jerin makaurata. Yanzu, gamayyar kasa da kasa ta riga ta mai da hankali ga batun nan.

Batun Makaurata ya riga ya zama mawuyacin batu ga kasa da kasa. Bisa sabuwar kididdigar da aka yi, an ce, yanzu, yawan makaurata na duk duniya ya kai miliyan 185, daga cikinsu, makauratan Afrika sun fi yawa, a wajen kasashe masu fama da talauci kuma mutanensu da suka taba samun horon fasahohi da yawa kamar su likitoci da masu aikin jiyya sun kaura zuwa sauran kasashe, wannan ya sa wadannan kasashe sun rasa kwararru da yawa, kuma suna karancin 'yan kwadago. Amma a wajen kasashen da suka karbi makauratan, su ma suna gamu da babban kalubale a fannoni da yawa bisa sanadiyar shigar da makaurata da yawa, kamar batun hakkin dan Adam da rashin aikin yi da haduwar al'adu iri daban daban da dai sauransu. A bayyane ne, batun makaurata batu ne mai wuyar daidaituwa da gamayyar kasa da kasa ba ta iya kebantar da da shi ba.

Kasashe masu wadata ta yammacin duniya sun sha mugun tasiri bisa sanadiyar tsofaffin da ke kara yawa ke yi da tattalin aziki na duk duniya , a wasu sassansu, an yi karancin 'yan kwadago, kamar su, likitoci da manoma da masu aikin gine-gine da dai sauransu, saboda haka wadannan kasashe ba su sa kayadde shigar da makaurata ba. Yanzu, kasashe sai kara yawa suke suna son karbar makauratan da ke da fasahohi da kudadden jari da yawa.


1  2  3