Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-06 16:07:38    
Bayani game da Wang Xuan, mashahurin masanin kimyya na kasar Sin

cri

Farfesa Wang Xuan ba kullum yake zama cikin ofishinsa ba wato ya kan je ofisoshin yin gwaje-gwaje inda yake amsa tambayoyin da dalibansa suka yi masa a kowane lokaci, da himmantar da su wajen yin nazari.

Farfesa Wang Xuan ba ma kawai ya nuna kulawa ga samari wajen zaman rayuwarsu ba, har ma ya mai da hankali sosai kan ci gaban da suka samu wajen sana'o'insu. A yanayin rani na shekarar 1989, ya gaya wa dalibinsa Xiao Jianguo wanda ya sami ci gaba wajen binciken fasahar yin dabi cewa, ya kamata ya kara samun babban ci gaba, kuma dole ne ya samu fasahar tsara babbakun sinanci masu launi kan jaridu. Sakamakon himma da taimakon da ya bayar, kuma bisa kokarin da dalibi Xiao ya yi cikin shekara daya da 'yan watanni, a karshe ya haye wahaloli ya samu nasara wajen fasahar yin aikinsa.

Farfesa Wang Xuan ya dora muhimman bukatu ga kansa, amma ya nuna karamci ga jami'a da sha'anin binciken kimiyya. A shekarar 2002, ya ba da gudummawar kudin yabo na Yuan miliyan 9 da ya samu domin kafa "sabon asusun Wang Xuan na yin binciken kimiyya da sabunta fasaha" domin nuna goyon bayansa ga ayyukan bincike da ake yi cikin ofishin binciken injuna masu kwakwalwa. (Umaru)


1  2  3