Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-06 16:07:38    
Bayani game da Wang Xuan, mashahurin masanin kimyya na kasar Sin

cri

Lokacin da mugun labarin rasuwar Wang Xuan, madugun tsara babbakun Sinanci ta hanyar laisel, kuma dan cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin ya kai jami'ar Beijing, tarin abokan aikinsa da dalibansa sun yi bakin ciki kwarai sabo da sun rasa wani malami kuma shugaba mai kirki, suna tunawa da wannan masanin kimiyya sosai.

Farfesa Xiao Jianguo, dalibin farfesa Wang Xuan, kuma manajan rukunin Founder na jami'ar Beijing ya bayyana cewa, "muddin ka karanta littattafai da jaridu, muddin kuwa ka nuna masa godiya, daidai kamar ka gode wa masanin kimiyya Thomas Alva Edison a duk lokotan da kake yin amfani da wutar lantarki a kowace rana. Kowane littattafi da kowace jaridar da muke karantawa yanzu, dukkansu suna yin amfani ne da muhimmiyar fasahar da Malami Wang ya kago a wancan lokaci."


1  2  3