Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-06 16:07:38    
Bayani game da Wang Xuan, mashahurin masanin kimyya na kasar Sin

cri

Tun daga shekarar 1975, bisa matsayinsa na babban jami'in fasaha, farfesa Wang Xuan ya shugabanci aikin tsara babbakun Sinanci ta hanyar laisel da bincike da kuma tsara tsarin dabi da lantarki da aka yi daga baya. Da karfin zuciya ya zarce fasahar da Japan da Turai da Amurka suke da ita a wancan lokaci wajen yin dabi ta hanyar haske da cathode ray, kuma ya yi bincike da kuma tsara babbakun Sinanci ta hanyar laisel kai tsaye.

Kafin a samu fasahar tsara babbakun Sinanci ta hanyar laisel, an tsara babbakun Sinanci da darma har shekara da shekaru, aikace- aikacen da aka yi a da ba su tafiya yadda ya kamata, ma'aikata sun sha wahaloli da yawa wajen aiki, kuma aikin ya jawo kazamcewar muhalli sosai. Daga baya Farfesa Wang Xuan ya yi kirkira wadda ta sami iznin mallaka a fannoni da yawa, har ya kubatar da kasar Sin daga wahalar da ta sha har shekaru fiye da 100 wajen yin dabi da darma, an sami babbar fa'ida wajen zaman al'umma da tattalin arziki.

Liu Qiuyun, tsohon shugaban ofishin binciken injuna masu kwakwalwa na jami'ar Beijing wanda ya taba zama mai ba da taimako ga farfesa Wang yana tune da cewa, a duk lokutan da ofishin ya ba da kudin yabo, shugaba Wang Xuan na ofishin ya kan ba da kudin yabo na musamman ga samari wadanda suka samu ci gaba wajen nazari da ba da fifitattun taimako wajen yin bincike. Domin samun kwararrun samari da suke aiki cikin ofishin, farfesa Wang shi kansa ya roki shugaban jami'ir don yin matukar kokarin daidaita matsalar samun gidajensu da sauran abubuwan jin dadinsu.


1  2  3