Bayan da kasar Sin ta kulla huldar diplomasiyya tsakaninta da kasar Fiji a watan Nuwamba na shekara ta 1975, an gudanar da dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu lami lafiya, kuma jamlar cinikayya da ke tsakanin bangarorin biyu ta samu karuwa cikin sauri sosai. Ya zuwa yanzu, a cikin dukkan kasashen tsibirorin da ke kan kudancin tekun Pacific, kasar Fiji wata muhimmiyar abokiya ce ta kasar Sin wajen cinikayya. A cikin shekara ta 2005, jimlar cinikayya tsakanin kasashen Sin da Fiji ta kai dala miliyan 45.27, wato ke nan ta karu da kashi 16.9 cikin dari idan an kwatanta shi da na makamancin lokaci na shekara ta 2004.(Kande Gao) 1 2 3
|