Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-06 10:32:24    
Kasar Fiji, kyakyawar kasar tsibirai mai wadata

cri

Kasar Fiji wata kyakyawar kasar tsibirai ce da ke tsakiyar kudu maso yammacin tekun Pacific, murabba'in kasar ya kai fiye da kilomita dubu 18. Kasar Fiji tana kunshe da tsibirai 332, guda 106 da ke cikinsu ana iya samun mazauna a kansu. Birnin Suva, babban birnin kasar Fiji wuri ne mai ni'ima sosai, kuma shi cibiyar siyasa ta kasar da kuma tushe ne na sha'anin tufafi na duk kasar, ban da wannan kuma birnin shahararriyar tashar jiragen ruwa ce da ke kan kudancin tekun Pacific.

Tun fil azal, 'yan kabilar Fiji suna da zama a kan wadannan tsibiri, tun farkon karni na 19 turawa sun fara kaura gidajensu zuwa wurin. A cikin shekara ta 1874, 'yan Birtaniya sun fara yin wa Fiji mulkin mallaka. A ran 10 ga watan Oktoba na shekara ta 1970, kasar Fiji ta samu 'yancin kanta. A ran 27 ga watan Yuli ne shekara ta 1998, an gudanar da sabon tsarin mulkin kasar Fiji, kuma an canja sunan kasar zuwa Jamhuriyyar kasar tsibiran Fiji. Yawan mutanen kasar Fiji ya kai dubu 868, ciki har da 'yan kabilar Fiji da yawansu ya kai kashi 51 cikin dari da kuma 'yan kabilar India da yawansu ya kai kashi 44 cikin dari. 'yan kasar Fiji suna bin addinan Kirista da India da kuma Musulunci. Harsunan gwamnatin kasar su ne Turanci da harshen Fiji da kuma harshen India, kuma dukkan 'yan kasar suna iya Turanci.


1  2  3