A cikin dukkan kasashen tsibirori da ke kan kudancin tekun Pacific, kasar Fiji wata kasa ce da aka raya tattalin arzikinta cikin sauri. Gwamnatin kasar Fiji tana mai da hankali a kan raya tattalin arziki na kabilun kasar da ingiza zuba jari da kuma sayar da kayayyaki ga kasashen waje. Sha'anin samar da sukari da na yawon shakatawa da na sarrafa tufafi su muhimman sha'anoni ne na tattalin arzikin kasar Fiji. Sabo da kasar Fiji ta samar da rake da yawa, shi ya sa a kan kira kasar da suna "tsibirin sukari".
Daga shekaru 80 na karni na 20, gwamnatin kasar Fiji ta fara bunkasa sha'anin yawon shakatawa bisa yanayinta mai kyau. Ya zuwa yanzu, kudaden shiga da aka samu daga sha'anin yawon shakatawa ya kai kashi 20 cikin dari na dukkan jimlar kudade da kasar ta samu wajen samar da kayayyaki. A cikin duk kasar Fiji, mutane kusan dubu 40 suna aikinsu a cikin hukumomin yawon shakatawa, wanda ya kai kashi 15 cikin dari na dukkan masu neman samun aikin yi na duk kasar. A cikin shekara ta 2004, masu yawon shakatawa na kasashen waje da suka zo kasar Fiji don yin ziyara ya kai sau dubu 507, kudaden shiga wajen yawon shakatawa ya kai kusan dala miliyan 450.
1 2 3
|