
A ran 4 ga wata da dare, firayim ministan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Thailand Thaksin Shinawatra ya yi jawabi a kan talijibin, inda ya bayar da sanarwar cewa, ba zai zama firayim minista a cikin sabuwar gwamnatin kasar ba.
An haifi Thaksin a birnin Chiangmai na kasar Thailand a ran 26 ga watan Yuli na shekara ta 1949. A cikin shekara ta 1973, ya samu sukolashif da gwamnatin kasar ta bayar, sabo da haka ya je kasar Amurka domin neman kara ilminsa. Daya bayan daya ne ya gama karatunsa daga jami'ar Eastern Kentucky da jami'ar Houston ta kasar Amurka bayan da ya samu digiri dakta da kuma digiri na biyu kan ilmin shari'a.
1 2 3
|