Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-04 17:06:31    
A yi yawon shakatawa a birnin Tianjin na kasar Sin

cri

Lalle, haikalin Confucius ba makaranta ba ne a yanzu, amma ya zama wuri ne da ake yin yawon shakatawa, ko ake dudduba bikin sadaukarwa da ake yi ga Confucius. Yanzu a ko wace shekara, a kan shirya gagarumin biki a haikalin Confucius na birnin Tianjin don yin sadaukarwa ga Confucius a yanayin bazara da na kaka wato lokacin haihuwar Confucius da rasuwarsa. Idan wani dan yawon shakatawa ya yi sha'awar manyan al'adun gargajiya na kasar Sin, to, ko shakka babu, zai yi kallon bikin sadaukarwa da ake yi wa Confucius.

A wani wuri da ke daf da haikalin Confucius na birnin Tianjin, an gina wata husumiyar inda aka ajiye babbar ganga a karni na 14. Da Madam Yi Hua, mataimakiyar shugabar ofishin kula da husumiyar ganga ta birnin Tianjin ta tabo magana a kan tarihin husumiyar nan, sai ta bayyana cewa,

"bayan da sojoji mahara na taron dangi na kasashen mayaudara guda 8 suka kutsa kai da hari cikin birnin Tianjin a shekarar 1900, sai aka rushe ganuwar birnin a shekarar 1901. Ko da yake husumiyar ganga ta birnin ba a rushe ta ba, amma an lahanta ta kwarai. Bayan haka an yi babbar kwaskwarima a kanta ne a shekarar 1921, ta haka an kara kayatar da wannan husumiyar ganga har ba a taba ganin irinta ba a da. Amma a sakamakon ci gaba da ake ta samu wajen raya birnin Tianjin tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, an rushe wannan husumiyar ganga a shekarar 1952 yayin da ake fadada hanyoyin mota a cikin birnin. Don yadada al'adun gargajiya a birnin Tianjin, an sake gina wannan husumiyar ganga a shekarar 2000 kuma a wurin da take a zamanin da."


1  2  3