Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-04 17:06:31    
A yi yawon shakatawa a birnin Tianjin na kasar Sin

cri

Birnin Tianjin yana kudancin birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. In an tashi daga birnin Tianjin zuwa birnin Beijing cikin mota, sai an yi wajen awa 1. Birnin Tianjin wani tsohon birnin al'adu ne, yau sama da shekaru 600 ke nan da aka gina shi. A nan, akwai wasan kwaikwayo na Opera na birnin da zane-zanen gargajiya da a kan yi don barka da sabuwar shekara da tsoffin kayayyakin al'adu iri daban daban. A farkon farko, za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan haikalin Confucius a birnin Tianjin.

An gina haikalin Confucius a wurare daban daban na kasar Sin. Dalilin da ya sa haka shi ne domin a nan ne a kan yi sadaukarwa ga Confucius, shahararren masani a fannin tunani da ilmi. Haka nan kuma haikalin Confucius manyan makarantu ne da aka kafa a wurare daban daban. Bisa kidayar da aka yi, an ce, yawan haikalan Confucius da aka kafa ya zarce 2,000 a duk duniya, daga cikinsu akwai haikalan Confucius sama da 300 wadanda aka kare su sosai a yanzu. Haikalin Confucius na birnin Tianjin yana daya daga cikin wadannan haikalai.

Haikalin Confucius na birnin Tianjin manyan tsoffafin gine-gine ne wadanda suke nan sumul garau. Madam Chen Tong, mataimakiyar shugabar ofishin nunin haikalin Confucius na birnin Tianjin ta bayyana cewa, za a kara fahimtar hanyar da aka bi a zamanin da don neman sanin zaman jami'ai ta ziyarar haikalin Confucius. Ta ce, "babu yadda za a yi a sami damar zaman jami'ai a zamanin da, sai an yi karatu a makaratun gwamnati wato haikalin Confucius. Idan wani ya ci jarrabawa har ya zama na farko a cikin jarrabawar da aka yi a duk kasar Sin, to, zai sami damar zama babban jami'in gwamnati mai hannu da shuni. "


1  2  3