
A wani fanni daban kuma, sassan kula da yanayin samaniya na kasar Sin kuma sun yi ta bunkasa ayyukan yin hidima wajen rage yawan bala'o'in halittu na yanayin samaniya, nan gaba kuma za su yi shirin kara yin hidima ga kauyuka da unguwoyin birane da masana'antu wajen yanayin samaniya.
Mr. Xu Xiaofeng, mataimakin shugaban hukumar yanayin samaniya ta kasar Sin ya bayyana cewa,
"Cikin shekaru 5 masu zuwa wato a lokacin da ake tafiyar da shiri na 11 na shekaru 5 na raya kasar Sin, muna son kara yawan tashoshi masu aiki da kansu wajen duba yanayin samaniya wato yawansu zai kai fiye da dubu 30 a kasar Sin, yawancinsu kuma za a kafa su ne a wurare masu nisa da kauyuka." (Umaru) 1 2 3
|