Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-24 17:08:47    
Kasar Sin ta dukufa kan kara daga matsayin yin hidima wajen ba da labarin yanayin samaniya tun kafin lokaci

cri

"Kowace rana da safe da kuma dare, nakan sauraron labaru game da yanayin samaniya a daidai lokaci ta kafofin watsa labaru, musamman ma ga labaru game da bala'o'in halittu ciki har da guguwa, sassa daban-daban na birnin Shanghai sukan ba da irin wadannan labaru daga duk fannoni, wannan ya ba ni sauki wajen yin zaman rayuwa".

Kasar Sin tana fuskantar wahaloli da yawa sabo da bala'o'in hailittu, a sa'i daya kuma kullum tana ta yin kokarin kafa da kuma kyautata tsarin yin bincike da sa ido domin rage yawan mugun tasirin da bala'o'in halittu suka jawo mata. Bisa abubuwan da Qin Dahe, shugaban hukumar yanayin samaniya ta kasar Sin ya gabatar an ce, yanzu kasar Sin ta riga ta kafa cikakken tsarin duba yanayin samaniya daga duk fannoni, ta yadda za a iya kara yin hidima da kyau ga mutane wajen samar musu da labarun jan kunne kan yanayin samaniya a daidai lokaci kuma bisa gaskiya, da kuma kara karfin duk zaman al'umma wajen fama da bala'o'in halittu, da yin namijin kokari domin kiyaye kwanciyar hankali na jama'a a fannin rayuka da dukiyoyinsu. Mr. Qin ya ce,

"Yanzu kasar Sin tana da tashoshin duba yanayin samaniya wadanda yawansu ya kai kusan 4000 wadanda kuma suke barbazuwa ko'ina a duk kasar Sin baki daya. Kasar Sin kuma ta zama kasa ta 2 wato bayan Amurka wajen kafa tsarin duba yanayin samaniya na zamani da ake kira Doppler Weather Radar, yawan irin wannan Radar da kasar ta kera ya kai kusa da 100, ban da wannan kuma taurarin dan adam na yanayin samaniya mai suna "Fengyun 1 da Fengyun 2" suna nan suna zagaya duniya lami lafiya".


1  2  3