A ran 23 ga wata ranar yanayin samaniya ce ta duniya, babban take na ranar wannan shekara shi ne "yin rigakafi da rage bala'in halitta". Bisa matsayinta na wata kasar da takan samun bala'o'in yanayin samaniya, kasar Sin kullum tana kokarin daga matsayin yin hidima wajen ba da labarin yanayin samaniya tun kafin lokaci, ta kan ba da labarun jan kunne kan yanayin samaniya a daidai lokaci, kuma ta ba da gudummawa domin rage mugun tasirin da ake gamuwa da shi sabo da bala'o'in halittu. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.
Shekarar da ta wuce wata shekara ce wadda bala'o'in halittu na yanayin samaniya suka faru har sau da yawa a Shanghai, birnin masana'antu da kasuwanci da ke bakin teku na gabashin kasar Sin, yawan labarun jan kunnen mutane da tashar yanayin samaniya ta birnin ta bayar tun kafin lokacin tashin guguwa da zafin yanayi da kasaitaccen hazo ya kai 56. Mr. Zhou Lin, dan birnin Shanghai ya ce, sabo da haka ba zai iya rabuwa da labarun da aka bayar kan yanayin samaniya cikin zaman rayuwarsa ba. In ji shi,
1 2 3
|