Idan ana so a raya wasannin motsa jiki a cikin kauyuka na duk kasar Sin, dole ne gwamnatin kasar ta kara zuba jari da goyon baya. Sabo da haka, Zhang Faqiang, dan majalisar CCPCC kuma mataimakin shugaban babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya gabatar da shawarar cewa, sabo da kudin da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ke da shi yana da yawa yanzu, shi ya sa ya kamata a kara zuba jari ga kayayyakin motsa jiki na kauyuka. Bisa labarin da ya samu, an ce, a cikin shekarar da muke ciki, kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare ga harkokin kasar Sin yana cikin shirin zuba jari na miliyan 30 domin gina kayayyakin motsa jiki na kauyuka, kuma ya ba da shawara ga babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin da ta ba da wasu kudaden tambola domin ba da taimako ga sha'anin motsa jiki na kauyuka.
Kudi yana da muhimmanci, amma manufofi sun fi muhimmanci. Yayin da gwamnatin kasar Sin ta tsara shirin ayyuka na shekaru 5 masu zuwa, ta dora muhimmanci kan karfafa samar da kayayyakin motsa jiki na kauyuka da kuma kara raya ilmi da kiwon lafiya da al'adu na kauyuka. (Kande Gao) 1 2 3
|