A farkon watan Maris, a nan birnin Beijing, an yi taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC. A gun taron, batun noma da kauyuka da manoma ya jawo hankulan 'yan majalisar sosai kamar yadda aka yi a lokacin da. Amma bambanci shi ne ba da dadewa ba gwamnatin kasar Sin ta bayar da wani fayil kan gina sabbin kauyuka na gurguza, ban da wannan kuma a cikin rahoton da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi, ya dora muhimmanci kan manufofi da matakai na goyon bayan bunkasuwar sha'anin noma da kauyuka. Wakilan jama'ar Sin da 'yan majalisar CPPCC su ma sun ba da shawarwari kan gina sabbin kauyuka. Daya daga cikinsu shi ne karfafa wasannin motsa jiki a kauyuka.
Ana iya gane bambancin da ke tsaknin birane da kauyuka a fannoni daban daban na zamantakewar al'umma, ciki har da wasannin motsa jiki. Ko da yake yawancin 'yan wasan Sin mafiya nagarta sun zo ne daga kauyuka, amma wasannin motsa jiki ba shi da farin jini a kauyuka. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba a iya samun isassun kayayyakin motsa jiki da kudi a kauyuka ba, bugu da kari kuma manoma su kan sha aikin noma sosai. Chen Yaobang ya fadi haka ne. Mr. Chen ya taba zama ministan noma na kasar Sin, yanzu shi shugaba ne na kungiyar wasannin motsa jiki na kauyukan kasar Sin.
1 2 3
|