Amma manoman Sin masu aiki tukuru sun nuna gwanintarsu wajen haye wahalolin rashin filaye da kayayyaki na motsa jiki. Chen Yaobang ya bayyana cewa, a cikin kauyuka masu yawa, manoma sun motsa jiki bisa wuraren da suke ciki, wato sun hada kayayykin motsa jiki da kayayyakin samar da albarkatun kasa tare. Alal misali, a cikin jihar Hubei, manoma sun hada filin kwallon kwando da filin busar da amfanin gona tare. Yayin da manoma suke shan aiki, sai su yi amfani da filin don busar da shuke-shuke, yayin da manoma ba su da aikin yi, sai su yi amfani da filin don yi wasan kwallon kwando.
1 2 3
|