Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-23 16:16:37    
Aikin kiyaye wurare masu damshi da ake yi a kasar Sin

cri

Wurare masu damshi suna nufin fadamun da ke da ruwan dadi ko ruwan gishiri, da wurare masu tabo da gawayi ko masu ruwaye na halitta ko na dan Adam na duk shekara ko na lokaci-lokaci bisa sauyawar yanayi, ciki har da ruwan tekun wanda zurfinsa bai wuce mita 6 ba. Wurare masu damshi da koramu da tekuna su ne manyan tsare-tsaren halittu guda 3 na duniya, wadanda suke da amfanin kiyaye mafarin ruwa, da kyautata ingancin ruwa, da tattara ruwa domin yin maganin fari, da kyautata yanayin sama da kuma kiyaye ire-iren halittu masu rai.

Kasar Sin tana da albarkatun wurare masu damshi da yawa, fadinsu ya kai matsayi na farko na Asiya, kuma ya kai matsayi na 4 na duniya. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2004 an ce, jimlar fadin wurare masu damshi wadanda kowanensu ya kai fiye da kadada 100 da ake da su a kasar Sin ta kai kadada miliyan 38.48, amma ban da Hongkong da Macao da Tiawan na kasar Sin.

Mr. Cao ya ce, tun dogon lokacin da ya wuce, sabo da rashin sanin da aka yi kan wurare masu damshi wadanda suke kan wani muhimmin matsayi wajen tsarin halittu, ana ta killace wurare masu damshi don gina gonaki ko yi musu gyare-gyare a makance, muhallin halittu na wadannan wurare yana ta lalacewa, kuma an sami zaizayewar ruwa da kasa, da tattarar kasa da rairayi a wadannan wurare, ban da wannan kuma akan aiwatar da wadannan wurare fiye da kima wato ba bisa gaskiya ba, shi ya sa fadin wurare masu damshi na kasar Sin yana ta raguwa.


1  2  3