Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-23 16:16:37    
Aikin kiyaye wurare masu damshi da ake yi a kasar Sin

cri

Kwanan baya majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yarda da "Tsarin tafiyar da aikin kiyaye wurare masu damshi na duk kasar" wanda a ciki aka tsai da cewa, daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, kasar Sin za ta ware kudin Sin Yuan biliyan 9 domin kiyaye albarkatun wurare masu damshi wadanda yawansu sai kara raguwa yake a kowace rana.

Cao Qingyao, kakakin hukumar gandun daji ta kasar Sin ya bayyana cewa, wannan ya alamanta cewa, an fara aikin kiyaye wurare masu damshi na kasar Sin da gaske. Ya ce, bisa wannan tsari an ce, za a yi amfani da wadannan kudade wato Yuan biliyan 9 domin yin muhimman ayyukan guda 4 wato kiyaye wurare masu damshi da farfado da su da aikin ba da misalin koyo wajen yin amfani da wadannan wurare da kuma kara karfinsu wajen aiwatar da aiwatar da albarkatun kasa, zuwa shekarar 2010 kuma za a yi kokarin samun sakamakon kiyaye muhimman wurare masu damshi da yawansu ya kai kashi 70 bisa 100 na kasar, kuma za a kafa wani tsarin kiyaye wurare masu damshi na halitta.


1  2  3