Wannan malamarta ta bayyana cewa, dole ne 'yan wasa su fid da tsoro su fuskanci 'yan kallon wasanninsu, saboda haka gasar wasanni ta zama jarrabawar da aka yi ga dukan 'yan wasa bisa matakin koli. Bisa himmar da malamarta ta yi mata ne, tana kan hawan dakalin nuna wasanni don shiga gasar da aka shirya wajen rera wakoki iri iri. Saboda haka , ta hanyar kokarinta, ta sami sakamako mai kyau wajen gasanni da yawa , kuma ta zama wata sabuwar tauraruwa wajen rera wakoki.
A shekarar 1990, Zabiya Zhang Huamin ta sami damar shiga kungiyar wake-wake da raye-raye ta rundunar soja ta kasar Sin da ke birnin Beijing daga birnin Xi'an, ta zama 'yar wasa da ke rera wakoki ita kanta a dakalin nuna wasanni.
Zabiya Zhang Huamin ta kan tafi tsaunuka masu tsawo sosai don rera wakoki ga sojojin da ke gadi a wadannan wurare tare da wahaloli da yawa, ta yi fama da mawuyacin halin da ake ciki, shi ya sa ta burge sojoji sosai da sosai, kuma sojoji da yawa sun yi mata godiya sosai , sun yi mata lakabi cewa, ita ce tsuntsun lark da ke rera wakoki masu dadin ji . (Halima) 1 2 3
|