Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-22 17:13:27    
Wata shaharariyar zabiya ta rundunar sojan kasar Sin

cri

Wakar tana da halin bayyanuwar farin ciki sosai da ake yi a lokacin murnar ranar biki, kuma waka ce ta soyayya mai kyau da samari maza da mata suke begen samuwa. Zabiya Zhang Huamin ta bayyana cewa, ta iya rera wakar da dadin ji, shi ne saboda tasirin da garinsa ya yi mata, ta kama hanyar nan ta rera wakoki ne bisa jagorancin mahaifiyarta . An haife ta a shekarar 1962 a wani gidan ma'aikaci a tsohon birnin Xi'an na lardin Shanxi, tun lokacin da take karama, sai ta bayyana hazikancinta wajen rera wakoki, lokacin da ta bayyana yadda take girma, ta bayyana cewa,

tun lokacin da na ke karama, na yi kishin rera wakoki sosai, duk saboda lokacin da mahaifiyata ta lalashi ni don shiga barci, ta rera mini wakoki, ina jin wakar da mahaifiyata ta rera na da dadin ji sosai, daga nan sai na soma son rera wakoki sosai.

Bayan da ta girma, tana son zama wata 'yar wasanni ko wata soja mai sanya suturar soja, a lokacin da ta cika shekaru 11 da haihuwa, ta taba koyon wasannin kwaikwayo na kasar Sin wato wasan Beijing Opera, sa'anan kuma ta koyi raye-raye a cikin shekaru da yawa.

A shekarar 1980, Zabiya Zhang Huamin ta shiga cikin wata gidan tiyatar nuna wasannin wake-wake da raye-waye ta lardin Shanxi, ta yi wa wata malamarta godiya sosai saboda taimakon da ta yi mata a lokacin da take girma.


1  2  3