Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-22 16:18:10    
Kasar Liberia ta bukaci kasar Nijeriya ta mika wa mata Charles Taylor tsohon shugaban kasar

cri

Ran 17 ga wata, sabuwar shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta tabbta cewa, gwamnatin Lebiria ta riga ta bukaci kasar Nijeriya ta mika wa mata Charles Taylor tsohon shugaban kasar Liberia. Ana tsamani cewa watakila Charles Taylor yana fuskantar da hukunci.

Shugaban kwamitin kula da harkokin zabe na kasar Liberia madamFrances Johnson-Morris ta bayyana a ran 15 ga wata cewa, kwamitin zai gabatar da sakamakon karshe na babban zaben shugaban kasar bayan da zai bi bahasin karar da aka kai game da zambar da aka yi cikin babban zaben shugaban kasar a wannan gami.

A ran nan wannan kwamitin ya tabbatar da cewa, bisa dukan kuri'un da aka kada cikin zagaye na 2 da aka kidaya, an ce, tsohuwar ministar kudi ta kasar madam Ellen Johnson-Sirleaf ta sami kuri'un da yawansu ya kai kashi 59.4 bisa dari, yayin da tsohon dan wasan kwallon kafa mafi nagarta na duniya da aka zaba a shekarar 1995 Mr. George Weah ya sami sauran kuri'un da aka jefa. Amma Mr. George Weah da masu goyon bayansa sun yi suka cewa, an yi zamba cikin babban zaben shugaban kasar, sun kuma bukaci sake gudanar da babban zaben shugaban kasar. Duk da haka ne wasu kungiyoyin kasa da kasa da ke kushe da Kawance Kasashen Afirka da Kawancen Kasashen Turai sun yi nuni da cewa, an gudanar da wannan babban zaben shugaban kasar cikin adalci da 'yanci kuma a fili.


1  2  3